Me ya sa Rasha ke ɗaure masana kimiyya a ƙasar? - BBC News Hausa (2024)

Me ya sa Rasha ke ɗaure masana kimiyya a ƙasar? - BBC News Hausa (1)

Asalin hoton, Reuters

Bayani kan maƙala
  • Marubuci, Sergei Goryashko
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Russian

A ko wane lokaci shugaban Rasha Vladimir Putin kan yi ikirarin cewa kasarsa ce kan gaba wajen samar da makamai masu gudu kamar walkiya.

Sai dai a shekarun baya an tuhumi wasu masana kimiyya da laifin cin amanar kasa, inda aka kai su gidan yari, lamarin da kungiyoyin kare hakkin bil'Adama ke kallo a matsayin wuce gona da iri.

Yawancin wadanda aka kama din dattawa ne, kuma uku daga cikinsu sun rasu, yayin da gudan aka dauke daga gadon asibiti a lokacin da yake tsananin jinyar cutar sankara, inda ya rasu ba da jimawa ba.

Akwai kuma Vladislav Galkin, dan shekara 68, wanda gidanshi ke Tomsk a kudancin Rasha,an kai samame gidansa a watan Afrilu, 2023.

Wasu mutane sanye da bakaken kaya, sun rufe fuska da mayafi ne suka kai samamen, inda suka bincike gidansa tare da kwashe wasu takardunsa da ke dauke da wasu bayanan kimiyya masu mahimmanci, cewar wani makusancinsa.

Matar mista Galkin, Tatyana ta ce ta sanar da jikokinsa da suke buga wasa da shi cewa ya yi tafiyar kasuwanci. Ta kuma ce ma'aikatar tsaron Rasha ta hana ta yin magana kan lamarin.

Me ya sa Rasha ke ɗaure masana kimiyya a ƙasar? - BBC News Hausa (2)

Asalin hoton, Kolker family

A shekarar 2015, an kama masanan kimiyya guda 12 wadanda suke da alaƙa da kimiyyar makami mai gudu kamar walƙiya. Dukkaninsu an tuhumesu ne da laifin fitar da bayanan ƙasa ga ƙasashen waje.

An riƙa yin zaman shari'arsu a asirce, saboda haka ba a samu bayanan haƙiƙanin laifin da ake tuhumarsu da shi ba.

Gwamnatin Rasha ta ce ba za ta ce komai ba sai dai kawai sun aikata gagarumin laifi. Amman abokanan aikinsu da lauyoyi sun ce an same su ne da laifin ƙera makamai da kuma hadin guiwa da kasashen waje.

Sai dai masu suka na ganin cewa kawai jami'an tsaron Rasha sun fake da haka ne saboda kawai su nuna wa duniya cewa wasu kasashe na bibiyar sirrin yadda ƙasar ke ƙera makamai.

Me ya sa Rasha ke ɗaure masana kimiyya a ƙasar? - BBC News Hausa (3)

Asalin hoton, Getty

Abinda ake nufi da makami mai gudu kamar walkiya shi ne makamai masu linzami waɗanda za su iya yin tafiya cikin sauri sosai kuma suna canza alkibla yayin tashin jirgin, da kauce wa duk wata na'urar da ke kakkabo makamai.

Rasha ta ce ta yi amfani da nau'i biyu a yaƙinta da Ukraine.

Sai dai Kyiv ta ce dakarunta sun harbo wasu makamai masu gudu kamar walkiya na Rasha, lamarin da ya sanya ayar tambaya kan ƙarfinsu.

Jim kadan bayan kama Mista Galkin, an gurfanar da shi a gaban kotu a rana daya da wani masanin kimiyya, Valery Zvegintsev, wanda suka yi hadin gwiwa tare da rubuta takardu da dama.

Kamfanin dillancin labaran kasar Tass ya ambato wata majiya mai tushe na cewa mai yiwuwa an kama Mista Zvegintsev ne sakamakon wani labarin da aka buga a wata jarida ta Iran a shekarar 2021.

Me ya sa Rasha ke ɗaure masana kimiyya a ƙasar? - BBC News Hausa (4)

Asalin hoton, Tomsk Polytechnic Institute

An wallafa sunan mista Galkin da mista Zvegintsev a jaridar a matsayin wadanda ke taka rawa wajen ƙera makamai masu gudu kamar walƙiya.

A shekarar 2022, jami'an tsaron Rasha sun ƙara kama wasu mutum biyu abokan aikin Mista Zvegintsev wanda ke aiki a wata cibiyar samar da makamai masu gudu kamar walƙiya.

Me ya sa Rasha ke ɗaure masana kimiyya a ƙasar? - BBC News Hausa (5)

Asalin hoton, ITAM

"Batun makami mai gudu kamar walƙiya ya zama wani batu da ke tilasta mutane zuwa gidan yari," in ji Yevgeny Smirnov, lauya a wata kungiyar kare hakkin bil'Adama da shari'a ta Rasha.

Mista Smirnov ya kare masana kimiyya da sauran wadanda ake zargi da laifin cin amanar kasa a gaban kotu kafin ya tashi daga Rasha zuwa Prague a shekarar 2021, saboda fargabar kada gwamnati ta yi masa wani abu.

Me ya sa Rasha ke ɗaure masana kimiyya a ƙasar? - BBC News Hausa (6)

Asalin hoton, Bauman Moscow State Technical University

Vladimir Lapygin, na da shekara 83, an daure shi a shekara ta 2016 amma an sake shi bayan shekara hudu.

Ya yi aiki na tsawon shekara 46 a babbar cibiyar bincike ta hukumar sararin samaniya ta Rasha, TsNIIMash.

An yanke wa Lapygin hukunci kan kunshin bayanin wata manhaja da ya aika zuwa ga wani abokin hulɗarsa ɗan ƙasar China. Ya ce ya aika da bayanan ne a matsayin wani bangare na tattaunawa game da yiwuwar sayar da cikakken bayanan a madadin cibiyar.

Ya kuma ce bayanan ba su ƙunshi wasu bayanan sirrin ƙasa ba,

Lapygin ya shaida wa BBC cewa duk wadanda aka kama ba su da alaƙa da ƙera makamai.

Me ya sa Rasha ke ɗaure masana kimiyya a ƙasar? - BBC News Hausa (7)

Asalin hoton, Getty

"Akwai rikici a harkar"in ji wani abokin aikin ɗaya daga cikin wadanda aka kama, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa.

Ana son masana kimiyya su riƙa wallafa wa duniya su gani, su kuma hada ƙarfi da sauran masana kimiyya na wasu ƙasashen, "A ɓangare guda kuma hukumar tsaron Rasha na ganin hakan a matsayin cin amanar ƙasa", in ji shi.

"Abin da aka karrama mu a kansa yau, zai iya zama dalilin da za a daure mu gobe."

Me ya sa Rasha ke ɗaure masana kimiyya a ƙasar? - BBC News Hausa (8)

Asalin hoton, Lefortovo court press service

Wani tsohon jami'in tsaron Rasha Janar Alexander Mikhailov ya ce "dole ne hukumar tsaron Rasha ta tabbatar da tsaron bayanan ƙasa."

Ya kuma ce yana da yaƙinin cewa ba za a yankewa wani hukuncin zmana gidan yari har na tsawon shekara 14 ba tare da an same shi da ƙwaƙwaƙwaran laifi ba.

"Wasu suna da surutu da yawa wanda za ka samu sun fitar har da bayanan da bai kamata ba."

Dangane da Mista Galkin, yanzu sama da shekara guda kenan da jami'ai masu rufe da fuska suka kai samame gidansa, inda ya kuma shafe wata uku a gidan yari, in ji wani ɗan uwansa.

Tatyana, matarsa, ta ce tana iya magana da shi ta wayar tarho irin wadda ake yi a gidan yari wato ta bayan gilashi. Kuma ta yi tunanin ita ma kawai ta ce su kamata, " Saboda lokaci yana ta tafiya yana can shi kadai."

"Zan iya roƙonsu su saka ni a cikin gidan da ake tsare da shi kafin a yi shari'a."

Ƙarin wasu masanan da Rasha ta kama

  • Alexander Shiplyuk, mai shekara 57, darakta a kamfanin ITAM, An kama shi a 2022, wanda har yanzu ke zaman shari'a.
  • Alexander Kuranov, tsohon dirakta a ci biyar bincike ta makamai masu gudu kamar walƙiya ta St Petersburg, an kama shi a 2021, an yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara bakwai a watan Afrilu, 2024.
  • Roman Kovalyov, abokin aikin Vladimir Kudryavtsev a TsNIIMash, an yanke masa hukunci zaman gidan yari na shekara bakwai a 2020, sai dai ya mutu a shekarar, 2022.
Me ya sa Rasha ke ɗaure masana kimiyya a ƙasar? - BBC News Hausa (2024)
Top Articles
Latest Posts
Article information

Author: Chrissy Homenick

Last Updated:

Views: 6377

Rating: 4.3 / 5 (54 voted)

Reviews: 93% of readers found this page helpful

Author information

Name: Chrissy Homenick

Birthday: 2001-10-22

Address: 611 Kuhn Oval, Feltonbury, NY 02783-3818

Phone: +96619177651654

Job: Mining Representative

Hobby: amateur radio, Sculling, Knife making, Gardening, Watching movies, Gunsmithing, Video gaming

Introduction: My name is Chrissy Homenick, I am a tender, funny, determined, tender, glorious, fancy, enthusiastic person who loves writing and wants to share my knowledge and understanding with you.